Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Jamhuriyar Congo: Kananan yara 400,000 na iya mutuwa saboda yunwa

Daya daga cikin kananan yara 'yan gudun hijira a Jamhuriyar Congo mai fama da yunwa, yayin duba lafiyarsa a wani asibiti. 5 Maris, 2018.
Daya daga cikin kananan yara 'yan gudun hijira a Jamhuriyar Congo mai fama da yunwa, yayin duba lafiyarsa a wani asibiti. 5 Maris, 2018. REUTERS/Thomas Mukoya
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Asusun tallafawa kana-nan yara na Majalisar Duniya UNICEF, ya ce yara 400,000 sun fuskantar hadarin rasa rayukansu a dalilin tsananin yunwa, muddin ba’a dauki matakai na gagawa ba.

Talla

Asusun na UNICEF ya dora alhakin gagarumar matsalar akan kazamin yakin da ake gwabzawa tsakanin sojin kasar ta Jamhuriyar da kuma ‘yan tawaye a lardin Kasai.

Majalisar dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa sama da mutane miliyan daya da dubu dari uku ne suka tsere daga yankin na Kasai tun bayan fara wannan yaki a watan Agustan shekarar 2016.

Rahoton majalisar ya ce dubban iyalan da suke tserewa gidajensu a halin yanzu na fama da rashin isasshen abinci da ruwa, dalilin da ya jefa su cikin munin yanayi.

Jimillar yaran da ke fama da rashin samun abinci mai gina jiki sun kai 770,000, daga cikinsu ne kuma 400,000 ke fuskantar hadarin hallaka muddin basu samu taimakon gaggawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.