Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan shi'a sun jikkata 'yan sanda a Abuja

Mabiya Shi'an dai sun yi ta jifan jami’an ‘yansandan da duwatsu inda su ke daga sauti kan lallai fa a saki jagoran na su Ibrahim Yakubu Zakzaky.
Mabiya Shi'an dai sun yi ta jifan jami’an ‘yansandan da duwatsu inda su ke daga sauti kan lallai fa a saki jagoran na su Ibrahim Yakubu Zakzaky. REUTERS/Stringer
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Wani dandazon mabiya Shi’a da ke zanga-zanga kan bukatar sakin jagoransu Ibrahim Yakubu Zakzaky da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da tsare da shi kusan shekaru 3, sun farwa jami’an ‘yansandan da ke Sakateriyar gwamnatin Tarayya a Abuja babban birnin kasar.

Talla

Jami’an ‘yansandan dai sun yi yunkurin dakatar da mabiyan na Shi’a wadanda suka rika amfani da dutsuna wajen yin jifa baya ga tare hanyoyi da kuma yunkurin lalata motocin Jama’a.

Rahotanni sun ce mabiyan sun rufe manyan hanyoyin da za su sada jama’a da fadar gwamnatin kasar mai karancin tazara da sakatariyar matakin da ya tilasta ‘yansandan daukar mataki.

Mabiyan dai sun yi ta jifan jami’an ‘yansandan da duwatsu inda su ke daga sauti kan lallai fa a saki jagoran na su Ibrahim Yakubu Zakzaky.

Kamfanin dillacin labaran Najeriyar NAN ya ce tuni wasu jami’an ‘yansanda na musamman suka isa wajen bayan mabiya Shi’an sun raunata babban jami’in sashen kula da manyan laifuka na babbar Sakatariyar ‘yansandan lokacin da ya yi kokarin gabatar da jawabi garesu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.