Burundi

An gudanar da zaben shugaban kasa a Burundi

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi na kada kuri'arsa a zaben kasar da ke gudana
Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi na kada kuri'arsa a zaben kasar da ke gudana rfi

A yau Alhamis ne al’ummar kasar Burundi ke jefa kuri’arsu a zaben raba gardamar da zai iya ba wa shugaban kasar Pierre Nkurunziza damar rike jagorancin kasar har shekarar 2034. To sai dai ana kallon zaben a matsayin abinda ka iya kara fargabar da ake ta fadawar kasar cikin halin rudanin Siyasa da kuma tashin hankali mai nasaba da kabilanci.

Talla

Tun kamin kawo karshen wa’adin yin gangamin zabe a kasar ta Burundi, da kusan ana iya cewar kasar Rwanda ce kadai kasar da ta fi ta fuskantar rudanin siyasa da ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa a shekarun baya, ‘yan adawar kasar suka koka akan yadda shugaban matasa na Jam’iyya mai mulki, ke barazanar kamawa da kashe duk wani da ke ganin ka iya karawa da shugaban kasar.

Kusan dai al’ummar kasar rabin miliyan ne suka bar kasar tun bayan da Pierre Nkurunziza ya yi nasara a zaben da ya bashi damar dare shugabancin kasar a wa’adi na uku da aka gudanar a shekarar 2015.

A wani abin da masu lura da al’amurra suka kalla a matsayin gurbataccen yanayin Dimokradiyya a kasar, Sakataren jam’iyyar mai mulkin kasar ya gaya wa wani taron gangamin zabe a birnin Bujumbura a wannan Makon cewar, duk wadanda suka yi adawa da bukatar sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasar, su ne makiyan ci gaban kasar.

A wannan watan ma an dakatar da ayyukan wasu kafaifan watsa labarai da suka hada da na kassahen ketare guda biyu akan watsa wata hira da mahukuntan kasar ke ganin ka iya kawo rarrabuwar kawuna da tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.