Nijar-Mali

Mutane 17 ne suka mutu a kauyen Tillabery

Wani yankin jihar Tillabery da ake fama da rashin tsaro
Wani yankin jihar Tillabery da ake fama da rashin tsaro RFI/Sayouba Traoré

Wasu mahara kan babura dauke da mugan makamai sun kashe Fulani 17 a kauyen Aghay dake Inates yankin Tillabery a Jamhuriyar Nijar da kan iyaka da kasar Mali.

Talla

Harin da ya auku cikin daren jiya juma’a a dai dai lokacin da mutane ke shirin shan ruwa na dada saka mutanen wadanan yankunan cikin zulumi duk da kokarin da hukumomin ke yi na tabbatar da tsaro a wadanan yankuna da aka jima ana bayyana su a matsayin wurraren dake tattare da hatsari.

Mazauna yankin da suka hada da Zabarmawa, Fulani da Bugaje na kallon wannan hari a matsayin ramuwar gaya daga bugajen kasar Mali tun bayan wani hari da Fulani mazauna Aghay suka kai musu a ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata inda Fulani suka kashe Bugaje 16.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.