Burundi

Nkrunziza na gaf da cimma burinsa na tazarce karo na 4

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza yayin kada kuri'a a zaben raba gardama na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima. 17 ga watan Mayu, 2018.
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza yayin kada kuri'a a zaben raba gardama na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima. 17 ga watan Mayu, 2018. Reuters

Shugaban Burundi Pierre Nkrunziza, na gaf da samun nasara a zaben rabar gardamar kasar na yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima, wanda ka iya bashi damar zarcewa a karagar mulki a zuwa shekara ta 2034.

Talla

Sakamakon zaben da aka kidaya zuwa daren jiya juma’a ya nuna cewa mafi wadanda ke goyon bayan sauya kundin tsarin mulkin ke kan gaba a yankuna 14 daga cikin 18 da ke kasar.

A yankin kudancin Bururi da kuma babban birnin kasar Bujumbura inda jam’iyya mai mulki ta CNDD-FDD bata taba kada ‘yan adawa ba, a wannan karon ta lashe kuri’un da aka kada a zaben raba gardamar da kashi, 53 da kuma 51.

Zaben raba gardamar ya gudana ne shekaru uku bayanda Nkrunziza ya sake tsayawa zaben shugabancin kasar wa’adi na uku, wanda ya yi nasara, lamarin da haddasa kazamin rikicin siyasa a kasar, da yayi sanadin hallakar sama da mutane 1,200 tare da tilastawa wasu kimanin dubu 400, 000 tserewa gidajensu.

Masu sukar gudanar da zaben, sun ce matakin koma baya ne ga yarjejeniyar zaman lafiyar kasar ta Burundi ta Arusha, wadda ta kawo karshen yakin basasar kasar da aka gwabza a tsakanin shekarar 1993 zuwa 2006.

Daya daga cikin manyan batutuwan da yarjejeniyar ta fasalta shi ne, ba za a barwa wani bangare na kabilun Hutu da Tusti mulkin kasar ba fiye da tsawon shekaru 10, domin yiwa kowane bangare adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.