Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Hukumomin Congo na bukatar karin haske daga Faransa

Tambarin kungiyar kasashen dake amfani da harshen Faransanci ta OIF
Tambarin kungiyar kasashen dake amfani da harshen Faransanci ta OIF

Ministan harakokin wajen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ya bukaci samun karin haske daga jakadun kasashen Faransa, Rwanda da Angola dake kasar dangane da kalaman Shugaban Faransa da ya furta a lokacin da ya karbi bakuncin Paul Kagame Shugaban Rwanda a Faransa.

Talla

Hukumomin Congo na danganta kalaman Shugaban Faransa zuwa kasar su a matsayin wucce gona da iri, musaman gani ta yadda kasar ta Congo ke dar-dar da kasashen Rwanda da Angola .

Kasar Congo ta nuna damuwa, inda hukumomin suka bayyana cewa gani yawan masu amfani da harshen faransanci a kasar, kuma kasancewar kasar ta uku a Duniya a matsayin kasa da aka fi amfani da Faransanci, Shugaban Faransa bai shawarce su ba wajen daukar matakin nuna goyan bayan sa zuwa yar kasar Rwanda a takarar neman kujerar Shugabar hukumar kasashen dake amfani da harshen faransanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.