Burundi

Nkrunziza ba zai tsaya takara a 2020 ba

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza yayin kada kuri'a a zaben raba gardama na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima. 17 ga watan Mayu, 2018.
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza yayin kada kuri'a a zaben raba gardama na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima. 17 ga watan Mayu, 2018. rfi

Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya sanar da cewar ba zai tsaya takarar shekarar 2020 ba, duk da rade radin cewar sauya kundin tsarin mulkin da ya kaddamar zai bashi damar tsayawa takara.

Talla

Yayin da yake jawabi gaban magoya bayan sa da kuma jami’an diflomasiya, shugaba Pierre Nkurunziza, ya baiwa marada kunya wajen sanar musu da cewar ba zai yi amai ya tande ba, wajen sake takarar shugaban kasar, inda yake cewa wa’adin mulkin sa zai kare a shekarar 2020, kuma daga wannan babu sabuwar takara.

Jawabin shugaban na zuwa ne lokacin da ya sanya hannu kan dokar da ta tababtar da sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda zai iya bahsi damar cigaba da zama a karagar mulki har zuwa shekarar 2034.

Nkurunziza da ya bayyana kan sa a matsayin jagorar Jam’iyyar CNDD-FDD, yace zai yi jifa da kwallon magoro domin ya huta da kuda idan wa’adin sa ya kare, kuma zai goyawa duk shugaban da ak azaba baya.

Shirin shugaban na sauya kundin tsarin mulki ya haifar da rudani da kuma tashin hankali a cikin kasar, abinda ya kai ga rasa dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.