Turai

Belgium ta baiwa Jean Pierre Bemba mafaka

Jean-Pierre Bemba, Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo
Jean-Pierre Bemba, Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo REUTERS/Michael Kooren

Gwamnatin Belgium ta amince tsohon mataimakin shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo wanda kotun duniya ta sallama Jean-Pierre Bemba ya samu mafaka a kasar.

Talla

Ministan harkokin wajen Belgium Didier Reynders ya ce Bemba wanda tuni iyalensa ke zaune a kasar za a karbe shi, to sai dai ya ce Belgium za ta cigaba da bai wa kotun hadin-kai a game da duk wasu batutuwa da suka shafi tsohon madugun ‘yan tawayen MLC.

A makon da ya gabata ne kotun hukkunta masu manyan laifuka ta duniya ICC, ta soke hukuncin daurin shekaru 18 da ta yankewa tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba, bisa aikata laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.