Mali

Sojan Mali na da hannu a kisan mutane a garin Mopti

Garin Mopti dake tsakiyar kasar Mali
Garin Mopti dake tsakiyar kasar Mali Getty Images/Friedrich Schmidt

Ministan tsaron Mali ya ce binciken farko da aka gudanar, na tabbatar da cewa sojojin kasar na da hannu wajen kisan mutane 25 da aka gano kaburburansu a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar.

Talla

Gwamnatin Mali ta aike da tawaga da ta je domin binciken,

Tawagar kwararri, wadda ta gano cewa lalle akwai mutanen da aka kashe sannan kuma sojoji na da hannu a lamarin,

Bayan gabatar da wannan rahoto, mataki na farko da hukuma ta dauka shi ne bai wa babban kwamandan askarawan kasa umarnin kai ziyara a yankin domin duba irin matakan da ya kamata a dauka a bangaren soji musamman hukunta wadanda ke da hannu a lamari.

Wannan na nufin cewa duk wanda aka tabbatar da cewa yana da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci kamar yadda ka’idar aikin soji ta tanada, sannan kuma ya fuskanci hukunci na shara’a.

Minista Tiena Coulibaly ya ce ko shakka babu za a hukunta wadanda aka sama da laifi wajen aikata wannan kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.