Isa ga babban shafi
Kasuwanci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin shekara ta 2018

Sauti 10:31
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da mataimakinsa Pr Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki.ntatives Yakubu Dogara.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da mataimakinsa Pr Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki.ntatives Yakubu Dogara. TheCable
Da: Abdoulkarim Ibrahim

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar na 2018 bayan  share dogon lokaci ana jiya.To sai dai a lokacin da yake rattaba hannu kan kasafin kudin, shugaba Buhari ya bayyana bacin ransa dangane da wasu sauye-sauye da majalisun kasar suka aiwatar dangane da ainihin abin da ya gabatar masu.Sauye-sauyen sun tanadi zaftare makuddan kudade da ya kamata a yi amfani da su domin gudanar da wasu muhimman ayyuka na cigaban kasar, yayin da 'yan majalisar ke cewa sun yi haka bisa tsari na doka. Shirin Kasuwa a Kai Maki Doli na wannan mako, Bashir Ibrahim Idris ya mana dubi ne game da wannan batu.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.