Najeriya-AU

Buhari zai halarci taron kungiyar AU a Mauritania

Muhammadu Buhari kusan za aiya cewa yayi kaurin suna wajen yaki da cin hanci da rashawa a nahiyar ta Afrika.
Muhammadu Buhari kusan za aiya cewa yayi kaurin suna wajen yaki da cin hanci da rashawa a nahiyar ta Afrika. NAN

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara shirye-shiryen barin kasar a yau Asabar inda zai tafi Mauritania don halartar taron shugabannin kasashen tarayyar Afrika AU da zai gudana. Taron na kwanaki 2 zai samu halartar kusan ilahirin shugabannin nahiyar dama wakilcin daga sassan duniya.

Talla

Sanarwar da fadar mulkin Najeriyar ta fitar ta bakin kakakin shugaban Femi Adesina ta ce Shugaba Buhari zai fara ziyarar ne daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli mai kamawa.

Taron wanda shi ne karo na 31 takensa shi ne nasara kan yaki da cin hanci da rashawa, kuma ana sa ran shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari shi ne zai gabatar da jawabin bude taro.

Yayin taron ana saran Muhammadu Buhari da takwarorinsa shugabannin Afrika za su yi wata ganawa ta musamman da shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda shi ma zai halarci taron.

Muhammadu Buhari kusan za aiya cewa yayi kaurin suna wajen yaki da cin hanci da rashawa a nahiyar ta Afrika, inda ko a taron kasashen da ya gudana baya bayan nan ya bukaci su kara kaimi wajen yakar matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.