Bakonmu a Yau

Awwal Musa Rafsanjani kan bukatar Buhari ga kasashen duniya wajen dawo da kudaden satar da aka ajje a can

Sauti 03:40
Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya su tallafawa na Afrika wajen dawo da kudaden da tsaffin shugabanninsu suka wawashe suka jibge a can.
Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya su tallafawa na Afrika wajen dawo da kudaden da tsaffin shugabanninsu suka wawashe suka jibge a can. REUTERS/Shannon Stapleton/File Photo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya da su saukakawa kasashen Afirka wajen ganin sun karbo makudan kudaden su da aka sace aka kuma boye a Turai. Buhari wanda shine shugaban yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka ya bayyana haka wajen taron shugabannin da yanzu haka ke gudana a Mauritania.Dangane da wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Awwal Musa Rafsanjani, Daraktan kungiyar Transparency International a Najeriya, kuam ga yadda hirar su ta gudana.