Isa ga babban shafi
Najeriya-Rashawa

Kotu a Najeriya ta sake bayar da belin Dasuki

Matukar dai gwamnatin Najeriyar a wannan karon ta amince da umarnin kotun na bayar da belin tsohon hafson tsaron, hakan zai kawo karshen daurewar da ake masa tsawon lokaci.
Matukar dai gwamnatin Najeriyar a wannan karon ta amince da umarnin kotun na bayar da belin tsohon hafson tsaron, hakan zai kawo karshen daurewar da ake masa tsawon lokaci. AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Wata Babbar Kotu a Najeriya ta sake bada belin tsohon Mai Baiwa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki beli akan kudi naira miliyan 100.Matukar dai gwamnatin Najeriyar a wannan karon ta amince da umarnin kotun na bayar da belin tsohon hafson tsaron, hakan zai kawo karshen daurewar da ake masa tsawon lokaci.

Talla

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bukaci gagauta sakin wanda ake zargin muddin ya cika sharuddan ba da belin.

Hukumar DSS ta kama ta kuma tsare Dasuki a watan Disambar shekarar 2015, inda ake tuhumar sa da laifin karkata da kudaden sayen makamai da suka zarce naira biliyan 2, zargin da yaki amincewa da shi.

Kotuna da dama sun bada umurnin sakin tsohon hafsan sojin amma hukumomin Najeriya sun ki aiwatar da hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.