Faransa-Najeriya

Macron na Faransa zai fara ziyara a Najeriya

Wannan ne dai karon farko da Emmanuel Macron zai kai ziyara Najeriyar inda zai yi wata tattaunawa ta musamman da shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Wannan ne dai karon farko da Emmanuel Macron zai kai ziyara Najeriyar inda zai yi wata tattaunawa ta musamman da shugaban kasar Muhammadu Buhari. rfi

A yau Talata ne ake saran shugaban Faransa Emmanuel Macron zai fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya wada za ta kai shi Abuja inda zai gana da shugaba Muhamamdu Buhari kafin zarcewa Lagos domin gudanar da wasu ayyuka.

Talla

Ziyarar ta Macron zuwa Najeriya na zuwa bayan kammala taron kungiyar kasashen Afrika a Mauritania wanda shugaban ya halarta.

Yayin taron na AU da aka shafe kwanaki biyu ana gudanarwa shugaba Macron ya yi ganawa ta musamman da wasu shugabannin kasashen nahiyar ta Afrika.

A jawabin da shugaban na Faransa ya gabatar a taron kungiyar ta AU ya ce za su aiki tukuru wajen ganin sun kawar da ta'addanci a yankin.

Wannan ne dai karon farko da Emmanuel Macron zai kai ziyara Najeriyar inda zai yi wata tattaunawa ta musamman da shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Najeriyar dai na daga cikin kasashen da ayyukan ta'addanci ya yi kamari a cikinsu babban kudirin shugabanta Muhammadu Buhari shi ne ganin ya yaki da ayyukan ta'addanci da kuma cin hanci da rashawa ba, haka zalika shi ma Emmanuel Macron babban kudirinsa ga kasashen na Afrika shi ne ganin an kawo karshen ayyukan ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.