IOM-LIBYA

'Yan cirani 1000 ne suka mutu a teku bana - IOM

Wasu 'yan cirani kenan da hukumar ta IOM ta ceto daga teku bayan kifewar kwale-kwalen da su ke ciki.
Wasu 'yan cirani kenan da hukumar ta IOM ta ceto daga teku bayan kifewar kwale-kwalen da su ke ciki. AFP/IOM

Hukumar kula da kaurar baki ta Duniya IOM ta ce akalla mutane sama da 1,000 suka mutu a cikin teku wannan shekarar a yunkurin su na tsallakawa Turai daga Libya domin samun rayuwa mai inganci.

Talla

Alkaluman da hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta bayar masu tada hankali ya nuna cewar mutane 204 suka mutu a cikin yan kwanakin nan sakamakon yadda masu safarar mutane suka cusa su a cikin kwale kwale marasa inganci dake tashi daga gabar ruwan Libya.

Othman Belbeisi, jami’in hukumar kula da kaurar bakin a Libya, ya ce akwai shaidun dake nuna karuwar mutanen dake mutuwa a kokarin su na tsallakawa zuwa Turai.

Kakakin hukumar, Leonard Doyle ya bayyana cewar karuwar bakin da ake samu wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa Turai yanzu na da nasaba da yanayi da kuma kammala azumin watan Ramadana.

Sai dai hukumar ta ce, duk da karuwar mutuwar da aka samu a cikin yan kwanakin nan, adadin mutanen da suka mutu a cikin wannan shekara bai kama kafar wadanda suka mutu a irin wannan lokaci bara ba.

Kasar Libya ta zama babbar hanyar da baki yan cirani ke amfani da ita wajen irin wannan tafiya mai dauke da hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.