Najeriya-Faransa

Buhari zai karbi bakoncin Macron na Faransa

Bayan kammala ganawa da Muhmmadu Buhari, Emmanuel Macron zai wuce birnin Lagos da ke kudancin kasar.
Bayan kammala ganawa da Muhmmadu Buhari, Emmanuel Macron zai wuce birnin Lagos da ke kudancin kasar. rfi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai karbi bakwancin takwaransa na Faransa Emmanuel Macron wanda zai yi ziyarar kwanaki 2 a kasar. Ana saran shugabannin biyu za su gana da juna tare da tattaunawa kan muhimman batutuwa ciki har da batun cin hanci da rashawa da kuma tsaro.

Talla

Emmanuel Macron wanda dama ya taba aiki da Ofishin jakadancin Faransa da ke Najeriyar shekaru 15 da suka gabata na ci gaba da daukar matakan ganin ya gyatta alaka tsakaninsa da kasashen renon Ingila inda ko a bara ya kai makamanciyar ziyarar zyarar Ghana.

Bayan kammala ganawa da Muhammadu Buhari a fadar Villa da ke Abuja babban birnin kasar, shugaba Emmanuel Macron zai wuce birnin Lagos da ke kudancin kasar don ziyartar fitaccen gidan rawar nan da shahararren mawakin Najeriyar Fela Anikulapo Kuti ya assasa.

Shugabannin biyu wadanda dama sun gana a Mauritania yayin taron kungiyar kasashen Afrika AU da ya gudana na da nufin kara dankon alakar da ke tsakaninsu musamman ta fuskar kasuwanci, tsaro da kuma yakar rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.