Kamaru-Zabe

Paul Biya na kamaru ya karawa kansa shekara guda a mulki

Shugaba Paul Biya ya ce matakin ya zama wajibi la'akari da cewa kasar ba za ta iya shirya zaben kafin karshen shekarar nan ba.
Shugaba Paul Biya ya ce matakin ya zama wajibi la'akari da cewa kasar ba za ta iya shirya zaben kafin karshen shekarar nan ba. LUDOVIC MARIN / AFP

Majalisar dokokin Kamaru ta kada kuri’ar amincewa da kara wa kanta shekara daya domin ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa bukatar shugaba Paul Biya.Matakin na Paul Biya na zuwa a dai dai lokacin da yawan 'yan kamaru de ke gudun hijira a makwabtan kasashen ke kara ta'azzara sakamakon tashe-tashen hankula a wasau sassan kasar.

Talla

Gwmanatin Paul Biya ta ce kara wa majalisar watanni 12 ya zama wajibi lura da cewa kasar ba za ta iya gudanar da zabubukan shugaban kasa, na ‘yan majalisar dokoki da kuma kananan hukumomi kafin karshen wannan shekara ba.

Kamaru dai na na daga cikin kasashen Afrika da ke fuskantar barazanar tsaro sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram da kuma rikicin 'yan aware da ke kara ruruwa a kowacce rana.

Tun kafin yanzu dai mahukuntan kasashe daban-daban ke fatan ganin Paul Biya ya mutunta bukatar ganin an gudanar da zaben kasar a karshen shekarar nan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.