Kamaru

'Yan Kamaru sun tara kudin tallafa wa yankin 'yan aware

Yankin Bamenda na Kamaru ya yi fama da rikicin 'yan arewa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama
Yankin Bamenda na Kamaru ya yi fama da rikicin 'yan arewa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama AFP/Reinnier KAZE

'Yan Kasar Kamaru da dama sun bada gudumawar kudade a wata gidauniyar taimaka wa mutanen yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi da rikici ya ritsa da su.

Talla

Gidan talabijin din gwamnati ya ce, akalla sama da rabin Cefa biliyan guda jama’a suka tara a birnin Douala cikin asusun gidauniyar.

Ranar 20 ga watan jiya, gwamnatin Kamaru ta sanar da shirin kashe Cefa biliyan 12 da rabi wajen tallafa wa mutanen yankin.

Rahotan gwamnati ya ce, 'yan awaren sun kashe jami’an tsaro 81 da fararen hula sama da 100, yayin da suka kona makarantu akalla 120.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.