Shugaban E. Guinea ya yi wa ilahirin fursunonin siyasar kasar afuwa

Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.
Shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema, ya amince da yin afuwa ga ilahirin fursunonin siyasar kasar afuwa, tare da sauran ‘yan adawa da gwamnati ta haramtawa gudanar da gangami ko wasu al’amuran siyasa a fadin kasar.

Talla

Matakin yi wa fursunonin siyasar afuwa na daga cikin sharuddan da ‘yan adawar kasar suka gindaya, kafin shiga tattaunawar sulhu da gwamnati wani lokaci cikin watan Yuli na shekarar 2018.

Gwamnatin Obiang ta ce babban makasudin aiwatar da shirin afuwar, shi ne bai wa dukkanin masu ruwa da tsaki a siyasar Equatorial Guinea musamman ‘yan adawa, damar shiga cikin tattaunawar warware rikicin siyasar kasar.

A halin yanzu dai shugaba Teodoro Obiang Nguema, shi ne wanda ya fi kowane shugaban kasa da ke kan mulki dadewa bisa karaga, bayan da ya shafe shekaru 39 yana jagorantar kasar tun daga shekarar 1979.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI