Bakonmu a Yau

Dakta Aliyu Idi Hong kan matsalar kai wa 'yan Najeriya hare-hare a Afrika ta Kudu

Sauti 03:39
Violence in South Africa has targeted foreigners Reuters/James Oatway/Sunday Times
Violence in South Africa has targeted foreigners Reuters/James Oatway/Sunday Times Reuters/James Oatway/Sunday Times

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yace yana daukar matakan da suka dace domin hukunta bata garin da suke kai hari suna kashe ‘yan Najeriya.Shugaban ya bayyana haka ne a Abuja bayan ganawar da suka yi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.A farkon shekarar 2018, cikin watan Janairu, wasu ‘yan bindiga suka kai hari unguwar ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudu tare da kone musu gidaje da shagunan kasuwanci a yankin Krugersdorp da ke gab da birnin Johannesburg.Kan wannan matsala ce Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Aliyu Idi Hong tsohon ministan harkokin wajen Najeriya.