Kamaru

Sojin Kamaru ne suka harbe fararen hula- Amnesty

Wasu sojojin Kamaru
Wasu sojojin Kamaru REUTERS/Joe Penney

Kungiyar Amnesty International ta ce, tana da shaidar da ke tabbatar ma ta cewar, sojojin Kamaru ne suka harbe fararen hular da yanzu haka ake yadawa a wani faifan bidiyo ta kafar sada zumunta.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce, binciken da masananta suka gudanar ya tabbatar mu su da cewar mutanen da aka gani cikin bidiyon sanye da kayan soji, sojojin gwamnatin Kamaru ne, lokacin da suke dirkawa ma ta biyu da yara kanana guda biyu harsasai.

Sai dai kakakin gwamnatin Kamaru, Issa Tchiroma Bakary ya bayyana bidiyon a matsayin na bogi, yayin da ya ce sun kaddamar da bincike akai.

Wannan hoton bidiyon da aka dauka da wayar hannu,  ya bayyana muryar wani  mai magana cikin harshen Faransanci da ke kiran sunayen mutanen akai-akai.

Bayan daure  fuskokinsu tare da tilasta musu tsugunawa, nan take sojin suka fara ruwan harsashai kan matan biyu da wata ‘yar karamar yarinyar, har ma da wani jariri a goye bayan uwarsa.

A cewar babbar jami’a a kungiyar kare hakkin bil’adama ta nahiyar Afirka REDHAC, Maximilienne Ngo Mbe, wannan hoton bidiyon, lallai dakarun tsaron Kamaru ne, kuma yankin Arewa mai nisa ne, in da sosoji ke fafatawa da mayakan Boko-Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.