Mali

Da sauran aiki zuwa hukumar zaben Mali

Taron mata dangane da zaben kasar Mali
Taron mata dangane da zaben kasar Mali ©RFI/Gaëlle Laleix

A Mali hukumar zaben kasar ta bayyana cewa daga cikin mutane milyan takwas da suka samu yi rijista, milyan uku ne suka samu damar karbar katunan zabe na shugaban kasar na ranar 29 ga wannan watan da muke cikin sa.

Talla

Shugaban tawagar yan sa ido daga kungiyar Tarrayar Turai a Mali ta bayyana cewa alkaluman da suke da su na nuni cewa akala kashi 12 cikin dari na mutanen da basu karbi katunan su ba na yankin kidal dake arewacin kasar, kashi 24 cikin dari daga Mopti a tsakiyar kasar sai kashi 53 cikin dari daga Sikasso dake kudu da birnin Segou.

Shugabar yan sa ido daga kungiyar tarrayar Turai Cecile Kyenge ta bayyana matukar damuwa gani salon da hukumar zaben ta yi amfani da shi wajen raba katunan zabe yayinda suka rage kwanuki 14 a gudanar da zaben kasar ta Mali.

Shugabar tawagar ta gamsu da yada yan takarar ke gudanar da yakin zaben su, ta kuma samu ganawa da yan takara 17 daga cikin yan takara 24 da ake da su a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.