Najeriya

Obasanjo yace yunkurin sa shine na ceto Najeriya

Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaban Najeriya
Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaban Najeriya

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yace babu abinda zai kauda hankalin sa a yunkurin da yake na ceto Najeriya daga rugujewa a karkashin gwamnatin APC dake mulki yanzu haka.

Talla

Yayin da yake karbar tawagar shugabannin Jam’iyyar PDP da suka je neman gafarar sa, Obasanjo yace a shirye yake ya baiwa duk wata jam’iyya shawara da take bukatar haka daga wurin sa.

Tsohon shugaban ya bukaci tawagar PDP da ta ziyarce shi da ta mutunta Jam’iyyun da suka shiga kawance da ita domin fuskantar zabe mai zuwa, kana da mutunta kudirin da suka sa a gaba.

Shugaban Jam’iyyar PDP Uche Secondus wanda ya samu rakiyar yan Majalisun gudanarwar Jam’iyyar da shugaban kwamitin amintattu Walid Jibrin ya ce abinda ya kai su wajen tsohon shugaban kasar shine neman gafara kan abinda PDP tayi masa da halin da Najeriya ke ciki a yau da bayani kan kawancen da PDP ta shiga da kuma kira ga Obasanjo cewar kar ya gaji da bada gudummawa domin ganin Najeriya bata ruguje ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.