Kabila zai fayyace matsayinsa kan zaben Jamhuriyar Congo

Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila.
Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila. © AFP

Shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, Joseph Kabila gobe zai yi jawabi ga al’ummar kasar a zauren majalisa, kasa da mako guda kafin fara rajistar ‘yan takarar zaben shugabancin kasar.

Talla

Sanarwar da Majalisun dokokin kasar guda biyu suka yi, sun nuna cewa shugaba Kabila zai gabatar da jawabi ne kan halin da kasar ke ciki.

Ana sa ran shugaban ya bayyana matsayin sa dangane da shirin gudanar da zabe da kuma yiwuwar sake tsayawarsa takarar, wadda tuni ta raba kan al’ummar kasar.

A makon jiya Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya soke ziyarar kasar domin bai wa Kabila damar bayyana matsayin sa kan shirin takarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI