Nijar

Faransa zata ci gaba da taimakawa bangaren tsaro a Nijar

Ministar tsaron Faransa a yankin Sahel
Ministar tsaron Faransa a yankin Sahel RFI/Olivier Fourt

Ministar Tsaron Faransa Florence Parly ta isa Jamhuriyar Nijar domin tattauna aikin rundunar sojin dake yaki da yan ta’adda ta G5 Sahel tare da takwaran ta Kalla Muntari na Nijar.

Talla

Ma’aikatan tsaron Faransa tace ziyarar zata karfafa dangantakar tsaro tsakanin Faransa da rundunar dake yaki da yan ta’addan sakamakon matsayin da kungiyar kasashen Afirka ta dauka a taro da ya gudana a Mauritania.

Jamhuriyar Nijar ke rike da shugabancin kungiyar tsaro ta G5 Sahel mai dauke da dakaru daga kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da Chadi da kuma Mauritania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.