Kamaru

An kashe shugaban coci a birnin Buea na kasar Kamaru

Shugaban Kamaru, Paul Biya.
Shugaban Kamaru, Paul Biya. AFP/Pool/Lintao Zhang

Wasu mutane da kawo yanzu ba a kai ga tantancewa ba, sun kashe shugaban cocin katolika a birnin Buea fadar gwamnatin daya daga cikin jihohin ‘yan aware da ke kasar Kamaru.

Talla

Mai magana da yawun cocin katolika a kasar ta Kamary ya tabbatar da labarin da ke cewa an kashe shugaban cocin mai suna Alexander Sob a cikin daren jiya juma’a.

Kafin wannan kisa dai tuni shugabannin cocin suka bayyana cewa ziyara zuwa yankunan ‘yan awaren abu ne mai wuya, sannan kuma wadanda ke rayuwa a can na cikin hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.