Nijar-Burkina

Ministar tsaron Faransa ta ziyarci Nijar da Burkina Faso

Ministar tsaron Faransa, tana ganawa da shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Ministar tsaron Faransa, tana ganawa da shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Twitter/ Florence Parly

Bayan da ta ziyarci birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar a jiya juma’a, daga bisani Florence Parly ministar tsaron Faransa ta wuce zuwa Burkina Faso daga daya cikin kasashen da ke fama da ‘yan bindiga a yankin Sahel.

Talla

Burkina Faso, daya ce daga cikin kasashen biyar da suka kafa rundunar G5-Sahel domin yaki da ayyukan ta’addanci a Sahel da suka hada da Nijar, Mali, Mauritaniya da kuma Chadi.

Faransa na daya daga cikin kasashen da ke taimaka wa rundunar da bayanan sirri, yayin da kasar ta jibge dimbin dakaru a yankin domin abin da ta kira yaki da ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.