Isa ga babban shafi
Kenya

Fira Ministan India ya bai wa marasa galihu kyautar Shanu 200

Fira Ministan India, Narendra Modi a kauyen Rweru na kasar Kenya, inda ya baiwa marasa galihu kyautar Shanu 200.
Fira Ministan India, Narendra Modi a kauyen Rweru na kasar Kenya, inda ya baiwa marasa galihu kyautar Shanu 200. REUTERS/Jean Bizimana

Fira Ministan kasar India, Narendra Modi ya bai wa wasu masarasa galihu da ke zaune a kauyen Rweru a kasar Kenya kyautar Shanu 200.

Talla

Modi ya bada wannan taimako ne yayin ziyarar da ya kai kasar ta Kenya a ranar Talata, kafin daga bisani ya tashi zuwa Afrika ta Kudu.

Kyautar Shanun ga marasa galihun ta karafafa wani shiri da kasar ta Kenya ta yi wa lakabi da Girinka, wanda ta kaddamar tun 2006, domin tallafa wa iyalan marasa karfi da Shanu, don bai wa ‘yaransu kanana damar samun isasshiyar madara.

Kalmar ‘Girinka’ a yaren Kenya na nufin ‘Ina yi maka fatan samun Shanu masu yawa’

Daga bisani Fira Ministan na India, ya bar Kenya zuwa Afrika ta Kudu, in da zai halarci taron tattalin arziki na 'BRICS' da ya kunshi kasashe biyar, da suka hada da China da Rasha da Brazil da Afrika ta Kudu da kuma India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.