Bakonmu a Yau

Farfesa Khalifa Dikwa kan yadda Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da salon mulkin Kamaru

Sauti 03:23
Majalisar Dinkin Duniyar ta yi zargin jami'an tsaron Kamaru da wuce gona da iri wajen azabtar da 'yan awaren kasar masu fafatukar ballewa.
Majalisar Dinkin Duniyar ta yi zargin jami'an tsaron Kamaru da wuce gona da iri wajen azabtar da 'yan awaren kasar masu fafatukar ballewa. REUTERS/Joe Penney

Shugaban Hukumar kare hakkin dan-adam na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra’ad Al Hussein ya kushe Gwamnatin Kamaru da Dakarun kasar saboda amfani da karfi fiye da kima don murkushe fararen hula wanda yasa mutane fiye da dubu 180 barin gidajensu a yankunan da ake amfani da turancin ingilishi.A kan haka Garba Aliyu Zaria ya nemi ji daga bakin Farfesa Khalifa Dikwa mai sharhi game da lamurran duniya dake zaune a Kaduna, yadda yake kallon wannan al’amari.