Najeriya-wasanni

NFF za ta fara bincike kan zargin kocinta Salisu Yusuf da rashawa

Mataimakin Kociyan Super Eagles Salisu Yusuf.
Mataimakin Kociyan Super Eagles Salisu Yusuf. Goal.com

Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta kaddamar da wani kwamitin bincike kan zargin karbar nagoro da ake yi kan mataimakin kociyan Super Eagles Salisu Yusuf.

Talla

Tun farko dai wani faifan bidiyo ne ya bankado asirin Kociyan lokacin da ya ke karbar wasu kudade a hannun wasu dillan ‘yan was biyu masu neman a saka ‘yan wasan nasu a manyan wasanni, ko da dai Yusuf ya ce adadin kudin bai wuce wanda hukumar FIFA ta haramta ba, haka zalika kudin da ya karba bai sanya shi saka ‘yan wasan biyu a wasanni da daillalan na su suka bukata ba.

Sanarwar daraktan yada labarai na NFF Ademola Olajire ta ce NFF za ta fara bincike tare da hadin Gwiwar kwamitin ladabtarwa don tabbatar da gaskiya kan zargin da ake yiwa kocin na ta.

Tuni dai tawagar masu horar da ‘yan wasa ta Najeriyar ta ce tana bayan shugaban na ta kasancewar bai aikata wani laifi da ya sabawa doka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.