Mai yiwuwa a haramtawa Jean-Pierre Bemba tsayawa takara

Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba
Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba REUTERS/Michael Kooren/File Photo

Jam’iyyar shugaba Joseph Kabila, mai mulkin Jamhuriyar Congo ta PPRD, ta ce mai yiwuwa ne tsohon mataimakin shugaban kasar, Jean-Pierre Bemba ya fuskanci haramcin tsayawa takarar shugaban kasa.

Talla

Kakakin jam’iyyar, Alain Atundu, ya ce Bemba ka iya fuskantar haramcin ne a karkashin dokar zaben kasar da ke haramtawa wadanda aka taba samu da laifukan cin hanci da rashawa tsayawa takara, dan haka suna fatan tsohon mataimakin shugaban kasar ya karbi kaddara, muddin haramcin ya tabbata a akansa.

A watan da ya gabata kotun ICC, ta wanke Bemba daga laifukan cin zarafin dan adam, da dakarunsa suka aikata a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sai dai har yanzu akwai hukuncin da kotun ta ICC ta yanke kansa a watan Maris na 2017, bisa zargin baiwa wasu shaidu cin hanci da ya yi.

A farkon watan Yuli na 2018 ne, kotun ta ICC ta bayyana yiwuwar yanke hukuncin daurin shekaru biyar kan Bemba, kan zargin cin hancin, sai dai har yanzu kotun bata tsayar da ranar zartas da hukuncin ba.

A ranar 1 ga watan Agusta ake sa ran komawar Jean-Pierre Bemba gida, bayan da jam’iyyarsa ta MLC ta sanar da zabensa a matsayin dan takararta na shugabancin kasar.

Har yanzu dai shugaban kasar Jamhuriyar Congo, Joseph Kabila, bai bayyana matsayinsa kan tsayawa takarar shugabanci, don neman karin wa’adi ba, a zaben da zai gudana a ranar 23 ga watan Disamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI