Yaduwar makamai na rura wutar rikicin Afrika ta Tsakiya - MDD

Wani mayakin kungiyar 3R, yayin nuna makaman da ya mallaka a garin Koui, da ke Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. 27 ga watan Afrilu, 2017.
Wani mayakin kungiyar 3R, yayin nuna makaman da ya mallaka a garin Koui, da ke Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. 27 ga watan Afrilu, 2017. REUTERS/Baz Ratner/File Photo

Wata tawagar kwararru ta majalisar dinkin duniya, ta ce fasakaurin makamai mafi akasari kirar Rasha, zuwa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya cikin wannan shekara, ya kara rura wutar rikicin kasar da ya shafe tsawon lokaci.

Talla

Tawagar ta Majalisar dinkin duniya, da ta wallafa rahoton a jiya Juma’a, ta ce ana fasa kaurin makaman ne, daga Sudan ta Kudu, abinda ya karawa mayakan ‘yan tawaye karfi.

A shekarun baya ne kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya baiwa Rasha izinin saidawa gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar kananan makamai, domin karfafa sojinta, bayan da kwamitin ya kakabawa kasar takunkumin haramta mata cinikin makamai, domin kawo karshen rikicin kasar da ya lakume rayuka da dama.

Tun a shekarar 2013 rikici ya barke a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a lokacin da mayakan ‘yan tawaye Muslmi na Seeleka suka kawar da shugabancin Fransuwa Bozize, abinda ya jawo martani daga ‘yan tawayen kirista na anti balaka.

Sai dai duk da zaben sabuwar gwamnati karkashin Faustin-Archange Touadera a 2016, da kuma tura dakarun majalisar dinkin duniya, har yanzu gwamnatin ba ta da iko da mafi akasarin sassan kasar.

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoton, gwamnatin Rasha ba ta ce komai ba dangane da wannan rahoto, zalika gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.