Eritrea

Eritrea da Somalia sun soma yunkurin gyara alaka

Shugaban Eritrea Isaias Afwerki (hagu) yayin da ya karbi bakuncin shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda zai shafe kwanaki uku yana ziyara a Asmara, babban birnin Eritrea. 28 ga watan Yuli, 2018.
Shugaban Eritrea Isaias Afwerki (hagu) yayin da ya karbi bakuncin shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda zai shafe kwanaki uku yana ziyara a Asmara, babban birnin Eritrea. 28 ga watan Yuli, 2018. Somalia/Handout/REUTERS

Shugaban Somalia Muhd Abdul Farmajo, ya kai ziyara kasar Eritrea a jiya Asabar, wanda a karon farko kenan aka samu hakan a shekarun baya bayan nan, bayan shafe tsawon lokaci kasashen basa ga mijici ga juna.

Talla

Ziyarar shugaban na Somalia, ta biyo bayan gayyatarsa da takwaransa na Eritrea, Izias Afwerki ya yi, domin tattaunawa kan maido da kyakkyawar alaka tsakaninsu.

Gwamnatocin Somalia da suka shude, sun dage bisa zargin Eritrea da taimakawa mayakan al-Shebaab da makamai, zargin gwamnatin kasar ta sha musantawa, inda kuma a waccan lokacin, ta ke mayar da zargin tallafawa kungiyar ta al-Shebaab kan kasar Habasha.

Bayan karuwar tsamin dangantaka tsakaninta da Habasha, a shekarar 2007, kasar Eritrea ta fice daga cikin kungiyar kasashen yankin gabashin Afrika, domin nuna bacin ranta, bisa shigar dakarun sojin Habasha cikin Somalia, domin murkushe mayakan al-Shebaab.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.