Najeriya

EFCC ta tsare mataimakin shugaban Majalisar Dattijan Najeriya

Mataimakin shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Mr Ike Ekweremadu.
Mataimakin shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Mr Ike Ekweremadu. NAN

Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC ta kame mataimakin shugaban Majalisar Dattijai kasar Mr Ike Ekweremadu.

Talla

Wasu majiyoyin labarai sun ce tun da misalin karfe 9 na safiyar yau Mr Ekweremadu ya isa Ofishin hukumar da ke babban birnin kasar Abuja amma kawo yanzu ba a sanar da Fitowarsa ba, kuma babu hakikanin lokacin da zai fito a yau.

Hukumar ta EFCC ta ce akwai wasu tarin tambayoyi da za ta yiwa mataimakin shugaban Majalisar ta Dattijai wanda ke matsayin mafi rike da babban mukami daga babbar jam’iyyar adawar kasar ta PDP.

A makon da ya gabata ne hukumar ta EFCC ta yi sammacin Mr Ike don amsa wasu tarin tambayoyi da ta ce yana da amsoshinsu.

Akwai dai tarin zarge-zarge kan Ike Ekweremadu ciki har da na mallakar wasu tarin kadarori a kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.