Najeriya

Gwamnan Sokoto a Najeriya ya koma Jam'iyyar PDP daga APC

Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal. dailypost

Gwamnan jihar Sokoto da ke yankin arewacin Najeriya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da sauya shekarsa daga Jam'iyya mai mulkin kasar ta APC zuwa babbar Jam'iyyar adawa ta PDP.

Talla

Tambuwal wanda yana daga cikin jiga-jigan jam'iyyar da suka taimakawa shugaba Muhammadu Buhari samun nasara a zaben kasar na 2015, ya ce rashin gamsuwa da salon mulkin shugaban ne ya tilasta masa komawa asalin jam'iyyarsa.

Wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Tambuwal ya ce kafin sanar da matakin sai da ya tuntubi al'ummar jiharsa wadanda suka bashi kwarin gwiwar sauya shekar.

A shekarar 2014 ne Tambuwal wanda tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriyar ne ya sauya sheka daga jam'iyyar ta PDP zuwa APC tare da rakiyar wasu gwamnoni 4.

Ficewar gwamnan na Sokoto na zuwa kwana guda bayan ficewar shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Abubakar Bukola Saraki tare da gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmad daga Jam'iyyar ta APC mai mulki zuwa babbar Jam'iyyar adawa ta PDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI