Isa ga babban shafi
Najeriya-Rashawa

Najeriya ta bankado badakalar Naira biliyan 62 a kamfanin Inshorar Ma'aikata

Tuni Ministan kwadagon kasar, ya ce duk wanda aka samu da laifi zai dandana kudarsa.
Tuni Ministan kwadagon kasar, ya ce duk wanda aka samu da laifi zai dandana kudarsa. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 5

Gwamnatin Najeriya ta bankado badakalar kudi da suka kai sama da Naira Biliyan 62 a hukumar inshoran ma’aikata na kasar da ake kira Nigeria Social Insurance Trust Fund, NSITF.A ranar 15 ga watan Fabararirun shekarar 2017 ne ministan kodago Chris Ngige ya nada komiti na musamman don gudanar da bincike kan harkokin da suka shafi kudin hukumar, bayan wani rahoto daga hukumar EFCC da ya bankado nuna wadaka da rashin bin ka’idoji wajen kashe kudin jama’a, da kuma zargin wasu manyan shugabannin NSITF da hannu dumu dumu a ciki.Tuni Ministan kwadagon, ya ce duk wanda aka samu da laifi zai dandana kudarsa. Wakilinmu Muhammed Sani Abubakar ya gudanar da bincike kan lamarin, kuma ga rahotan da ya aiko mana.

Talla

Najeriya ta bankado badakalar Naira biliyan 62 a kamfanin Inshorar Ma'aikata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.