Zimbabwe

MDD ta bukaci 'yan siyasar Zimbabwe su kai zuciya nesa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci bangarorin siyasar Zimbabwe da su kai zuciya nesa, biyo bayan tarzomar da ta barke a kasar saboda zargin magudin zabe.

Wasu magoya bayan jam'iyyar adawa ta MDC a Zimbabwe, yayin shirin arrangama da wasu jami'an sojin kasar, yayin da suke zanga-zangar adawa da sakamakon zaben shugaban kasa. 1 ga watan Agusta, 2018.
Wasu magoya bayan jam'iyyar adawa ta MDC a Zimbabwe, yayin shirin arrangama da wasu jami'an sojin kasar, yayin da suke zanga-zangar adawa da sakamakon zaben shugaban kasa. 1 ga watan Agusta, 2018. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Zuwa yanzu dai wannan tarzoma, wadda ta faro daga gudanar da zanga-zanga tayi sanadiyar asarar rayukan mutane 3.

Ita kuwa kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International, ta bukaci gwamnatin Zimbabawe da ta kaddamar da bincike kan matakan da sojoji suka dauka na amfani da karfin da ya wuce kima wajen kai hari kan masu zanga zanga.

Kiran na Amnesty ya zo ne, bayan da gwamnatin kasar ta Zimbabwe, ta sha alwashin murkushe duk wani tashin hankalin da ka iya tasowa sakamakon korafin da ya biyo bayan sakamakon zaben da ake cigaba da bayyanawa, wanda ya nuna cewar Jam’iyyar ZANU PF ke da rinjaye a Majalisar kasa.

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya zargi kawancen jam’iyyun adawa da tinzira jama’a.

Mnangagwa ya nanata cewa tilas jam’iyyun adawa su baiwa magoya bayan su dake tada hankali umarnin barin kan tituna, saboda zaman lafiya ya dawo kasar.

Shi kuwa mai Magana da yawun Jam’iyyar MDC, Nkuleku Sibanda kokawa yayi kan rawar da sojoji suka taka wajen murkushe masu zanga zanga, inda ya ce ‘Yan Sanda ne ya dace su dauki matakin magance duk wani tashin hankali da aka samu saboda horan da suka samu.

A cewar Sibanda an horar da sojoji su kashe mutane ne lokacin yaki, to amma abin mamaki sai gashi a halin yanzu sojojin na amfani da karfi fiye da kima, tamkar fararen hula sun zama abokan gabar gwamnati.

Yayin da yake tsokaci kan tashin hankalin, shugaban tawagar masu sa ido daga kasashen Turai, Elmar Brok yace jinkirin da ake samu na bayyana sakamakon zaben na jefa shakku kan sahihancin sa.

Sai dai shugabar hukumar zaben kasar Pricilia Chugumba, tayi watsi da zargin magudi a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI