Zimbabwe

Yan Adawar Zimbabwe sun ki amincewa da sakamakon zaben kasar

Yan adawa a Zimbabwe sun ki amincewa da sakamakon zaben kasar
Yan adawa a Zimbabwe sun ki amincewa da sakamakon zaben kasar REUTERS/Mike Hutchings

Yan adawan kasar Zimbabwe sun ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana, wanda aka bayyana shugaba Emmerson Mnangawa a matsayin zababen shugaban kasa.

Talla

Kafin karanta sakamakon zaben, kakakin babbar Jam’iyyar adawa ta MDC, Morgan Kamuchi ya shaidawa manema labarai dake hukumar zabe cewar, sakamakon na bogi ne, kafin yan sanda suyi awon gaba da shi.

Akalla mutane 6 sojoji suka harbe har lahira sakamakon tarzomar da ta biyo bayan zaben, yayin da masu sa ido da kasashen duniya suka gargadi sojojin kasar kan amfani da karfin da ya wuce kima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.