Turai

Bakin haure 1500 suka mutu a teku

Kungiyoyin dake aiki tanttance yan gudun hijira da bakin haure
Kungiyoyin dake aiki tanttance yan gudun hijira da bakin haure FATHI NASRI / AFP

Wani rahoton bincike daga hukumar yan gudun hijira sama da yan gudun hijira hade da yan cin’ rani 1500 ne suka rasa rayukan su a kokarin su na tsallakawa daga tekun mediterrane zuwa Turai kama daga farkon shekarar nan zuwa watan yuli 2018.

Talla

Tsakanin watan yuni zuwa watan Yuli na wanan shekara ta 2018 hukumar ta bayyana cewa sama da yan cin’ rani 850 ne suka mutu a cikin teku.

Sai dai hukumar ta sanar da cewa akala mutane 60.000 suka samu tsallakawa, a karshe hukumar yan gudun hijra ta bukaci kara samun hadin gwiwa daga hukumomin kasashe domin zakulo kungiyoyi dake da hannu a safarar mutane tareda karbar makuden kudade daga jama’a domin tsallakawa da su,wanda hakan ya sabawa dokokin kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.