Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Salva Kiir ya yiwa daukacin 'yan tawayen Sudan ta Kudu afuwa

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da abokin hamayyarsa Riek Machar, sai kuma shugaban Sudan Omar Al-Bashir a tsakiyarsu bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a Khartoum.
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da abokin hamayyarsa Riek Machar, sai kuma shugaban Sudan Omar Al-Bashir a tsakiyarsu bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a Khartoum. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya sanar da yin afuwa ga daukacin ‘yan tawayen kasar da suka dauki makamai domin yakar gwamnatinsa, cikin harda jagoransu kuma babban abokin hamayyarsa Riek Machar.

Talla

A cewar shugaba Salva Kiir dokar yin afuwar ta fara aiki ne tun a ranar 8 ga watan Agustan da muke ciki na 2018.

Matakin yi wa daukacin ‘yan tawayen kasar afuwa ya zo ne kwanaki biyu, bayan da shugabannin biyu, wato Kiir da Machar suka rattaba hannu akan yarjejeniyar sulhu ta karshe, tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye.

Yarjejeniyar wadda shugaban Sudan Omar Al-Basheer ya jagoranci kafawa a birnin Kahrtoum, ta fayyace yadda bangarorin biyu za su rarraba mukaman gwamnatin Sudan ta Kudun.

Yarjejeniyar sulhun da aka cimma, ta baiwa jagoran ‘yan tawayen Sudan ta Kudu riek Machar damar komawa kasar kuma kan tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa, mukamin da ya rike a shekarar 2013, kafin daga bisani yakin basasa ya barke a watan Disamba na shekarar, bayan da shugaba Salva Kiir ya zarge shi da yukurin yi masa juyin mulki.

A halin yanzu dai ana sa ran gwamnatin hadin gwiwar Kiir Da Machar za ta cigaba da tafiyar da kasar, har tsawon shekaru 3, wadanda a cikinsu za a shirya gudanar da zabuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.