Najeriya-Dangote

Ginin matatar mai mallakin Dangote a Najeriya zai samu jinkiri

Wata majiya mai kusanci da Attajirin ta ce sai a shekarar 2022 ne za a iya fara amfani da katafariyar matatar man sabanin shekarar 2020 da aka tsara.
Wata majiya mai kusanci da Attajirin ta ce sai a shekarar 2022 ne za a iya fara amfani da katafariyar matatar man sabanin shekarar 2020 da aka tsara. Reuters/路透社

Aikin ginin katafariyar matatar man da Attajiri Aliko Dangote ke shirin kammalawa a Najeriya zai gamu da tsaikon da zai tilasta kara wa’adin kammaluwarsa da akalla shekaru 2 sabanin yadda aka tsara.Wata majiya mai kusanci da Attajirin ta ce sai a shekarar 2022 ne za a iya fara amfani da katafariyar matatar man sabanin shekarar 2020 da aka tsara. 

Talla

Shirin ginin Matatar man wanda Aliko Dangote ya yi fatan kammalawa a shekarar 2019 ta kuma fara aiki a 2020 zai zamo mafi girma a Nahiyar Afrika da aka shirya samar da shi a jihar Lagos da ke kudancin Najeriyar, a cewar majiyar za a jinkirta fara amfani da shi daga 2020 zuwa 2022.

Matatar ta Man fetur wadda Aliko Dangote fitaccen attajiri zai gina za ta rika samar da akalla ganga dubu dari 6 da hamsin kowacce rana, matakin da aka yi ittifakin zai mayar da Najeriyar matsayin mai fitar da tataccen man fetur maimakon mai shigo da shi, baya ga bunkasa tattalin arzikinta da kuma janyo karin abokanan cinikayya.

Aliko Dangote wanda ya yi kaurin suna ta fuskar samar da siminti a kaf nahiyar Afrika, ya yi fatan kammala katafariyar matatar man irinta ta farko a Afrika cikin 2019 ta kuma fara aiki a 2020 sai dai Babban Daraktan Rukunin kamfanin na Dangote, Devakumar Edwin ya ce bangarorin matatun iskar gas da na man dizel ba za su kammlu ba har sai zuwa karshen 2021, wanda kuma ke nuna cewa a sai a 2022 ne za a fara cin moriyarsu.

Sai dai Mr Edem ya bada tabbacin cewa an kammala samar da akalla kashi 95 na Injiniyoyin matatar haka zalika akwai kashi 90 na dukkanin kayakin aikin da ake bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.