Libya-'Yan cirani

Jami'an Libya sun ceto 'yan cirani 60 daga tekun Mediterranean

Libyan ce dai hanya mafi sauki ga 'yan ciranin da ke son tsallaka nahiyar Turai don samun rayuwa mai inganci.
Libyan ce dai hanya mafi sauki ga 'yan ciranin da ke son tsallaka nahiyar Turai don samun rayuwa mai inganci. REUTERS/Ismail Zitouny

Jami’an da ke kula da gabar teku a Libya sun ceto akalla ‘yan ci rani 60 ciki har da mata da kananan yara masu kokarin tsallakawa nahiyar Turai ta Tekun Mediterranean.

Talla

Kakakin hukumar da ke kula da gabar Tekun a Libya, Ayoub Gassim ya ce ‘yan ciranin da suka kunshi mata 19 da kananan yara 4 sun galabaita a cikin tekun na Mediterranean bayan lalacewar jirginsu a tsakiyar teku tun ranar Litinin.

A cewarsa Tuni suka bayar da kulawar da ta dace ga mutanen su 60 yayinda aka ba su matsuguni a sansanin ‘yan cirani da ke garin Zawiya.

Libya dai na matsayin hanya mafi sauki ga ‘yan ciranin da ke son tsallakawa Nahiyar Turai don samun ingantacciyar rayuwa, yayinda lamarin ya ta’azzara tun bayan hambarar da gwamnatin Mu’ammar Qaddafi a 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.