Isa ga babban shafi
Mali-Zabe

An kashe Jami'in zabe guda, an yi garkuwa da 3 a Mali

Wasu mutane kenan lokacin da su ke kan layi don kada kuri'arsu a zaben Mali zagaye na biyu.
Wasu mutane kenan lokacin da su ke kan layi don kada kuri'arsu a zaben Mali zagaye na biyu. REUTERS/Luc Gnago
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
2 Minti

Wasu da ake kyautata zaton mayakan jihadi ne sun hallaka wani babban jami’in zabe yayin zagaye na biyu na zaben Mali da ke gudana. Matakin na zuwa a dai dai lokacin da wasu rahotanni ke cewa wasu tsageru sun yi garkuwa da wasu karin jami'an zaben 3.

Talla

Lamarin wanda ya faru a rumfar zabe ta Arkodia da ke garin Tumbuktu na yankin arewacin kasar rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun isa rumfar da misalin karfe biyu na tsakar rana inda suka bukaci kowa ya daga hannunsa.

Wani ganau ya ce bayan da ‘yan bindigar su 6 suka yi wa rumfar zaben kawanya ne jami’in ya nemi guduwa inda suka harbe shi da bindiga kuma nan ta ke ya mutu.

‘Yan bindigar sun hana ko da mutum daya ya kada kuri’a a rumfar zaben.

Dama dai ana gudanar da zaben na yau ne bisa fargabar komi zai iya faruwa la’akari da yadda aka kame wasu tsageru 3 na kungiyar Commando da suka shirya kaddamar da hare-hare yau.

Haka zalika Ma'aikatar tsaron kasar ta tabbatar da sace wasu karin jami'an zaben kasar 3 wadanda suka ake zargin 'yan bindigar da aikatawa.

Zaben wanda shi ne zagaye na biyu da ake fafatawa tsakanin shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita mai shekaru 73 da kuma tsohon ministan kudin kasar Soumaila Cisse mai shekaru 68 kowannensu ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

Ko a zagayen farko na zaben barazanar tsaro ta tilasta kulle runfunan zabe da dama musamman a yankunan da mayakan jihadin ke da rinjaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.