Isa ga babban shafi
Tunisia

Tunisiya za ta sauya tsarin rabon gado na Islama

Shugaban Tunisiya Béji Caïd Essebsi
Shugaban Tunisiya Béji Caïd Essebsi FETHI BELAID / AFP
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Shugaban Tunisiya, Beji Caid Essebsi ya sanar da shirinsa na gabatar da wani kudirin doka ga Majalisar Dokokin kasar da zummar samar da daidaito tsakanin maza da mata wajen rabon-gado. Tuni dubban ‘yan kasar suka fara gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matakin, in da suka lashi takobin kare dokokin addinin Islama.

Talla

A halin yanzu dai, Tunisiya na aiki ne da tsarin shari’ar Musulunci wajen raban gadon, in da maza ke samun ninkin kason ‘yan uwansu mata.

Sai dai shugaba Essebsi ya ce, za su sauya wannan tsarin ta hanyar samar da daidaiton rabon gadon tsakanin maza da mata, face wani babban dalili da ka iya hana dokar aiki a wasu lokuta.

Essebsi ya ce, samar da hadin-kai tsakanin al’ummar Tunisiya, na daya daga cikin ayyukan da suka rataya a wuyansa, yayin da ake saran shigar da dokar cikin kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 2014.

Sai dai duk da wannan mataki na Essebsi, al’ummar kasaar na da damar barin rubutacciyar wasiya kan yadda suke son a kasafta dukiyarsu bayan mutuwarsu.

A bangare guda, kwamitin da shugaba Essebsi ya kafa, na bukatar dage haramcin madigo da luwadi a kasar da kuma kawo karshen hukunce-hukuncen kisa.

A shekarar da ta gabata ne, gwamnatin kasar ta kafa dokar haramta musgunawa mata, yayin da ta ba su damar auren mazajen da ba Musulmai ba duk dai da sunan ‘yancin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.