Isa ga babban shafi
Nijar

Ambaliyar ruwa za ta iya kawo mummunar illa a Agadez

Masallacin tarihi na jihar Agadez
Masallacin tarihi na jihar Agadez RFI/Bineta Diagne
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 min

Mahukunta a Agadez da ke Arewacin Jamhuriyar Nijar, sun yi gargadin cewa ambaliyar ruwa da ake fuskanta za ta iya kawo mummunar illa ga gidaje da sauran wuraren tarihi da aka gina kusan shekaru 700 da suka gabata a jihar.

Talla

Magajin garin Agadez Rissa Feltou, ya ce kawo yanzu ambaliyar ta yi barna mai tarin yawa, inda yanzu haka ake cigaba da neman wata motar daukar marasa lafiya da ruwan ya dauke da mutane biyu a cikinta.

A farkon damana mutane 22 suka mutu sakamakon ambaliyar da aka samu a Jamhuriyar Nijar bayan ruwan sama mai karfi wanda ya shafi mutane kusan 50,000.

Alkaluman da hukumomi suka bayar sun nuna cewa gidaje 3,000 suka rushe, yayin da eka sama da 4,000 na gonaki suka lalace.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI Ministan agajin gaggawa Lawan Magaji ya ce birnin Agadez na da wasu manyan duwatsu wadanda suke da akalla tsawon kilo mita 2 zuwa sama, wadanda daga nan ne idan aka samu saukar ruwan sama, ruwa ke gangarowa da karfin gaske lamarin da ke haddasa gagarumar ambaliyar ruwa ga duka karkarar da ya tarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.