Nijar-Mali

Alkaluma dangane da yan gudun hijira a Tillabery

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wasu alkaluma dangane da yawan yan gudun hijira da suka tsere daga wasu yankunan arewacin Mali kama daga farkon watan Janairu zuwa wannan lokaci.A wannan rahoto hukumar ta bayyana irin kokarin da jami’an ta ke yi dama irin kalubalen dake gaban ta.

Yan gudun hijira da suka tsere daga garin Gao na kasar Mali
Yan gudun hijira da suka tsere daga garin Gao na kasar Mali MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Kama daga farkon shekarar nan sama da yan gudun hijira 17.000 ne suka samu rijista daga hukumar dake kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Nijar.

Yan gudun hijira da aka sarin su tabarbarewar tsaro a wani yankin na kasar Mali ya tilastawa baro matsugunin su.

Jami’an dake bada kulawa zuwa yan gudun hijirar sun bayyana cewa kusan mutane 17.382 ne suka gudo domin cira da rayukan su daga hare-haren mayakan jihadi, banda haka mutanen da rikicin kabilanci ya tilasatawa canza wurin zama zuwa garuruwa a yankin Tillabery a cewar ofishin hukumar dake kula da ayukan jinkai na OCHA.

Hukumar ta bayyana adadin na yan gudun hijira zai iya karuwa mudin aka samu tashin hankali.

Majalisar Dinikin Duniya ta kiyasta cewa akwai wasu alkaluma dake nuna mata cewa mutanen kauyuka 74 dake kan iyaka da kasar Mali suke cikin shirin ko ta kwana.

Hukumar ta bayyana cewa dakarun dake aikin kasa da kasa da suka hada da Mali, Nijar, Burkina Faso, Mauritanie et Chad sun taimaka zuwa hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kan su domin kai dauki zuwa mutane 96.000 a karshen watan yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI