Jamhuriyar Congo

Rashin tsaro ya haifar da cikas ga ayyukan WHO a Jamhuriyar Congo

Wasu daga cikin jami'an lafiyar Jamhuriyar Congo da na hukumar WHO, a garin Beni da ke lardin Kivu yayin gudanar da atasayen kula da masu dauke da cutar Ebola.
Wasu daga cikin jami'an lafiyar Jamhuriyar Congo da na hukumar WHO, a garin Beni da ke lardin Kivu yayin gudanar da atasayen kula da masu dauke da cutar Ebola. REUTERS/Samuel Mambo/File Photo

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce hare-haren gungun ‘yan bindiga a Jamhuriyar Congo, musamman a lardin Kivu da ke arewacin kasar, yana haifar da cikas ga ayyukan jami’anta da ke kokarin isa yankunan aka samu karin wadanda suka kamu da cutar Ebola, da kuma yankunan da ake bukatar a bincika.

Talla

Hukumar ta WHO ta ce daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa yau ta tabbatar da sahihancin rahoton karin mutane 78 da suka kamu da cutar Ebola, inda zuwa yanzu 47 daga ciki suka hallaka a dalilin cutar.

Hukumar lafiyar ta kara da cewa a halin yanzu akalla mutane 1,500 ne ta ke fargabar ko sun kamu da cutar Ebolar, ko kuma sun cudanya da masu ita a lardin Kivu da ke arewacin Jamhuriyar Congo mai fama da kazamin rikicin gungun mayakan ‘yan tawaye.

Shugaban hukuamr ta WHO Tedros Adhanom ya ce tashin hankalin da lardin na Kivu ke fama da shi, ya tilastawa ma’aikatan lafiya, kauracewa wurare da dama, domin kauce fadawa daya daga cikin kungiyoyin mayakan ‘yan tawaye akalla 100 da ke lardin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.