Jamhuriyar Congo-Ebola

Ana fargabar mutane dubu 2 sun kamu da Ebola a Jamhuriyar Congo

Tuni dai hukumomi a kasar ta Jamhuriyar Congo suka fara daukar matakan kare sauran miliyoyin jama'ar da basu kamu da cutar ba, musamman a yankunan da aka samu barkewarta.
Tuni dai hukumomi a kasar ta Jamhuriyar Congo suka fara daukar matakan kare sauran miliyoyin jama'ar da basu kamu da cutar ba, musamman a yankunan da aka samu barkewarta. AFP Photo/Junior D. Kannah

Ana fargabar kusan mutane dubu biyu sun kamu da cutar Ebola a Jamhuriyyar Demokradiyar Congo bayan cudanyar da suka yi da mutanen da cutar ta yi sanadin mutuwarsu.

Talla

Cutar wadda ta kara barkewa ranar 1 ga watan Agusta, ta hallaka akalla mutane 49 kawo yanzu yayinda fiye da dubu biyu ke karbar kulawar lafiya sakamakon cudanyar da suka yi da masu fama da cutar ciki har da kananan yara.

Yanzu haka dai akwai akalla mutane 63 da ake yi wa gwaje-gwaje bayan ganin alamun cutar tattare da su, yayinda wasu kuma 27 aka tabbatar da kamuwarsu.

Hukumomi a kasar ta Congo dai sun dauki matakan wayar da kan al’umma don gujewa kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.