Jamhuriyar Congo-Ebola

Adadin wadanda suka mutu saboda Ebola sun kai 55 a Congo

FILE PHOTO: Congolese officials and the World Health Organization officials wear protective suits as they participate in a training against the Ebola virus near the town of Beni in North Kivu province of the Democratic Republic of Congo.
FILE PHOTO: Congolese officials and the World Health Organization officials wear protective suits as they participate in a training against the Ebola virus near the town of Beni in North Kivu province of the Democratic Republic of Congo. REUTERS/Samuel Mambo/File Photo

Ma’aikatar kiwon lafiya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, ta ce adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Ebola sun hai 55 a halin yanzu.

Talla

Alkawalumman da ma’aikatar lafiyar ta fitar, ta ce mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu na zaune ne a yankin Kivu ta Arewa, yankin da ke fama da rikici na tsawon shekaru, lamarin da ke kara haifar da tarnaki ga jami’an kiwon lafiya da ke kokarin isa ga wadanda suka kamu da cutar.

Yanzu haka dai hukumar lafiya ta duniya na ci gaba da kokari domin tabbatar da cewa cutar ba ta yaduwa zuwa sauran sassa na kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.