Saudiya

Ana gudanar da bukukuwan sallar layya a sassan duniya

Ragudanan Sallar Layya
Ragudanan Sallar Layya RFI/Ndiassé SAMBE

Musulmi a sassa daban daban na duniya na gudanar da bukukuwan babbar sallah ko kuma sallar layya, bayan da mahajjata suka sauka daga hawan Arafat.

Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na gudanar da bukukuwan sallar ne a garinsu na Daura da ke arewacin kasar, inda rahotanni ke cewa shugaban ya taka da kafa har tsawon mitoci 800 domin dawowa gida bayan kammala sallar ta idi.

A jihar Kano kuwa, rahotonni sun ce gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya yi amfani da wannan rana domin ‘yantar da wasu fursunoni da yawansu ya kai 170 daga gidan yarin Goron Dutse, tare da bai wa kowanne daga cikinsu Naira dubu biyar a matsayin kudin mota domin komawa garuruwansu.

To sai dai a makociyar Najeriya wato Jamhuriyar Nijar, sai a gobe laraba ne za a gudanar da bukukuwan babbar sallar ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.